Bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya samu mafi ƙanƙantar tagomashi idan aka kwatanta da sauran shekarun baya, tun bayan zuwan annobar korona, wadda ta jefa tattalin arzikin ƙasar cikin garari.
A cikin sanarwar da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar, tattalin arziƙin Najeriyar na cikin gida ya samu bunƙasa da kashi 2.74 cikin 100 a 2023 saɓanin kashi 3.10 da ya kai a 2022.
Rashin aikin yi kuma ya ƙaru da kashi 4.2 cikin 100 zuwa kashi 5 cikin 100 idan aka kwatanta shekarun biyu.
NBS ta ce an samu bunƙasar ɓangaren noma da kashi 2.10 cikin 100 daga ƙaruwar kashi 2.05 cikin 100 da ya yi a rubu’i na huɗu na 2022.