Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar 2025, a cewar rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).
Sanarwar da NBS ɗin ya fitar ranar Litinin, ta ce wannan ya zarta kashi 2.27 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2024.
Rahoton ya ce ɓangarorin da suka fi ba da gudummawa wajen haɓakar tattalin arziƙin sun haɗa da na ayyuka da kuma masana’antu.
A lokaci guda kuma an sabunta ƙididdigar GDP daga shekarar 2019, inda sabon adadin ya kai naira tiriliyan 205, a cewar shugaban hukumar ƙididdiga ta ƙasa, Adeyemi Adeniran.
Ya bayyana cewa sabon adadin ya ƙaru da kashi 41.7 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2014.
Adeniran ya ƙara da cewa sassa guda biyar da suka fi taka rawa wajen wannan ci gaban sun haɗa da: noman da kasuwanci da ɓangaren masana’antu da kamfononin sadarwa da kuma man fetur da iskar gas.