Mai tsaron ragar Arsenal, Arthur Okonkwo, ya koma SK Sturm Graz a matsayin aro na sauran kakar wasanni.
Kungiyar Arsenal ta tabbatar da hakan a wata sanarwa ta shafinta na yanar gizo ranar Litinin.
An dawo da Okonkwo daga aronsa a Crewe Alexandra kafin ya koma SK Sturm Graz.
Sanarwar ta Arsenal ta kara da cewa: “An dawo da Arthur Okonkwo daga aronsa a Crewe Alexandra kuma ya koma SK Sturm Graz a matsayin aro na sauran kakar wasa.
“Yarjejeniyar ta dogara ne da kammala ayyukan da aka tsara.”
Okonkwo, mai shekaru 21, ya riga ya buga wasanni 26 a dukkan gasa da Crewe Alexandra a kakar wasa ta bana.