fidelitybank

Arsenal ta kwace Kyaftin daga hannun Aubameyang

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kwace ragamar Kyaftin din kungiyar daga hannun dan wasan ta, Pierre-Emerick Aubameyang, sakamakon keta da’a, da ya yi.

An ajiye dan wasan mai shekaru 32 a wasan da suka doke Southampton da ci 3-0 a ranar Asabar, kuma ba zai buga wasan da West Ham za ta ziyarci Emirates ranar Laraba ba.

“Bayan saba masa na ladabtarwa a makon da ya gabata, Pierre-Emerick Aubameyang, ba zai ci gaba da zama kyaftin din kungiyar ba, kuma ba za a yi la’akari da shi ba a wasan da za su yi da West Ham United ranar Laraba”. inji Arsenal a cikin wata sanarwa.

“Mu na sa ran dukkan ‘yan wasanmu, musamman kyaftin din mu, su yi aiki da bin ka’idojin da muka tsara kuma muka yarda.”

A cewar The Athletic, Aubameyang ya dawo daga baya fiye da yadda aka amince da shi daga balaguron sirri da ya yi zuwa Faransa a makon da ya gabata, wanda daga baya ya tilasta masa barin daukar horo, saboda bukatar wuce ka’idojin coronavirus.

Haka kuma kociyan kungiyar Mikel Arteta bai bar Aubameyang ba, saboda nasarar da suka samu a Arewacin Landan da Tottenham a watan Maris kan batun ladabtarwa a lokacin da ya isa a makare, domin wani taron share fage.

 

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp