A ranar Lahadi ne Arsenal ta zama ta daya a teburin Premier, bayan ta doke Chelsea da ci 1-0 a Stamford Bridge.
Gabriel Magalhaes ne ya zura kwallo daya tilo da aka tashi a wasan wanda ya baiwa Gunners dukkanin maki uku a kan Chelsea.
Sakamakon wasan da suka yi da Chelsea na nufin kungiyar Mikel Arteta ta kasance a saman teburin gasar Premier da maki biyu a gaban Manchester City ta biyu.
Arsenal tana da maki 34 a wasanni 13 na gasar Premier, yayin da Man City ke da maki 32 daga wasanni iri daya.
Yanzu dai kungiyar ta Arewacin Landan za ta kara da Wolves a ranar Asabar mai zuwa a wasansu na gaba a gasar Premier.
Sai dai Arsenal za ta fara karawa da Brighton a gasar cin kofin EFL ranar Laraba.