Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun karrama dan Najeriya dan kasar Birtaniya Daniel Anjorin mai shekaru 14, wanda ya rasa ransa a wani hari da aka kai masa aka caka masa wuka ranar Talata.
Magoya bayan sun karrama Anjorin a wasan da Arsenal ta buga da Bournemouth a filin wasa na Emirates ranar Asabar.
Wani matashi mai suna Daniel Anjorin, mai goyon bayan Arsenal, an kai masa mummunan hari a wani titi da ke unguwar Hainault a Gabashin Landan, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa makaranta.
Lamarin ya kuma yi sanadin jikkata wasu hudu. An samu karɓuwa daga ko’ina cikin duniya, tare da gudummawar da ta kai £118,502 a cikin kwanaki biyu.