Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Kylian Mbappe, in ji Football Transfers.
Kwantiragin Mbappe na yanzu da PSG zai kare a bazara mai zuwa a 2024.
Arsenal ta yaba wa kyaftin din Faransa, inda suke tunanin ko za su aika tayin ga wakilan dan wasan ko a’a.
Sai dai mai yiwuwa PSG ta siyar da dan wasan mai shekaru 24 a wannan kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara ko kuma ta rasa shi kan cinikin kyauta a bazara mai zuwa.
A halin da ake ciki kuma, a wani ci gaba mai alaka, Chelsea a ranar Asabar ta tabbatar da daukar sabon dan wasan, Alex Matos.
Matos, mai shekaru 18, ya koma Chelsea ne daga kulob din Norwich City na Ingila.
Blues ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta shafinta na yanar gizo.
“Chelsea ta kammala siyan Alex Matos daga Norwich City.
“Barka da zuwa Chelsea, Alex!” Sanarwar ta Chelsea ta karanta a wani bangare.