Tsohon dan wasan baya na Manchester United, Gary Neville ya fadawa ‘yan wasan Arsenal da su daina tunanin cin gasar kofin Premier.
Ya ce yakamata kungiyar ta maida hankali wajen samun nasara a wasansu na gaba da Southampton.
Damar Mikel Arteta na lashe gasar Premier ya yi kadan a ranar Lahadi, bayan wasansu da West Ham United ya tashi 2-2.
An tashi kunnen doki da West Ham ya biyo bayan wani canjaras da Liverpool ta yi a satin daya gabata.
Suna da wasa da abokiyar hamayyarta Manchester City a karshen wannan watan wanda dole ne ta yi nasara ko kuma ta yi bankwana da kambun.
Arsenal za ta buga wasanta na kasa da Southampton a daren Juma’a kuma Neville, wanda ya shahara a gasar Premier, ya yi imanin cewa har yanzu Gunners na da kyakkyawar damar lashe gasar – idan suka bi shawararsa.
“Amma a yau, ina ganin Arsenal kawai na bukatar ta tabbatar sun murmure a daren Juma’a kuma su buga wasa daya a lokaci guda, su samu maki bakwai a gaba,” in ji Neville a Sky Sports.
“Ku yi aikinku a karawar da Southampton, ku dage, ku samu tazarar maki bakwai kuma wasan Manchester City a Etihad zai kasance wasa sau daya a rayuwa.”