Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya ce, yankin Arewacin kasar nan zai biya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamna Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Tinubu a Kano ranar Lahadi.
Jamâiyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Ahmed Bola Tinubu, ya ziyarci jihar Kano domin bude ofisoshin yakin neman zabensa.
Gwamnonin jihohin Kano, Jigawa da Zamfara ne suka tarbe Tinubu a ranar Asabar a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano tare da dubban magoya bayansa.
Da yake jawabi ga dimbin jamaâar da suka hallara, Gwamna Muhammad Badaru ya ce Tinibu ne kadai ya goyi bayan âyan takarar shugaban kasa biyar na Arewa.
“Tinubu shine abokin arewa daya tilo, ya goyi bayan yan takarar shugaban kasa biyar na arewa da suka hada da Shehu Shagari, Umar Musa Yar’adua, Atiku Abubakar, Nuhu Ribado da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.”
âDon haka lokaci ya yi da za mu biya kuma mun shirya, mu mutane ne masu gaskiya, muna mutunta alkawari kuma a shirye muke mu biya ku diyya kan abin da kuka yi wa Arewa.â
Gwamna Badaru, ya bukaci âyan Arewa da su fito su kada kuriâar zaben dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar All Progressives Congress APC a zaben 2023 mai zuwa.