fidelitybank

Arewa za ta biya Tinubu a ranar zabe saboda ya mara wa Buhari – Aminu Jaji

Date:

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta ce, Arewa za ta biya dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu sakamakon goyon bayan da ta bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Aminu Jaji, Daraktan tuntuba da wayar da kan jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC) na yankin Arewa maso Yamma, ya yi magana a ranar Alhamis.

A wajen kaddamar da kwamitin a Abuja, Jaji ya ce kuri’un da za su fito daga yankin Arewa maso Yamma ne za su tabbatar da wanda zai shugabanci kasar nan.

Basaraken ya bayyana kwarin gwiwar cewa tsohon gwamnan Legas zai zama shugaban kasa a 2023.

Dangane da sakamakon zabukan 2015 da 2019, Jaji ya yi imanin APC za ta kai ga nasara saboda farin jininta.

“Mafi kyawun abin da za mu iya yi shi ne mu mayar wa Tinubu wanda ya goyi bayan danmu, Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa sau biyu.

“Lokaci ya yi da za mu biya abin da sauran shiyyar suka yi wa ɗanmu; uba kuma abin koyi, Shugaba Buhari,” NAN ta ruwaito yana cewa.

Jaji ya ba da tabbacin cewa za a mara wa Tinubu baya ba tare da wani sharadi ba, amma ya kamata ya ba da tabbacin ci gaban Arewa.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp