fidelitybank

Aregbbesola ya goge sakon da ya wallafa a kan Tinubu bayan cece-kuce da aka yi

Date:

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya goge wani rubutu mai cike da cece-kuce a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana farin cikinsa kan kayar da gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Gboyega Oyetola, da dan takarar jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke ya yi a Jam’iyyar (PDP).

A wani sako da ya wallafa a Facebook ranar Lahadi, Aregbesola ya tabbatar da nasarar da Ademola Adeleke ya samu a kan Oyetola mai ci, ta hanyar sanya wata ayar Littafi Mai Tsarki.

Ya dai wallafa sakon ne da misalin karfe 8 na safe, bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta tabbatar da Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben kuma zababben gwamna.

Wannan magana dai ta yi kaca-kaca da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, domin ya nuna cewa Allah ya fi shi iko.

Ana zargin ministan ya dauki nauyin Alhaji Moshood Adeoti, tsohon sakataren gwamnati ne domin ya fafata da Oyetola a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Bayan nasarar Oyetola, Adeoti ya maka Oyetola kotu, inda ya nemi a soke shi, saboda rashin yin murabus da wuri daga kwamitin rikon jam’iyyar na kasa.

Yayin da kotu ta yi watsi da karar a ranar Alhamis, rahotanni sun ce Aregbesola ya bar kasar zuwa Amurka, inda ya nuna ba zai halarci zaben gwamnan Osun ba.

To sai dai bayan da aka yi ta cece-kuce kan rubutun da aka yi a Facebook, Aregbesola ya goge shi.

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp