Jami’an tsaro da ke tare da ayarin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a yammacin ranar Alhamis, sun yi arangama da ‘yan Shi’a a yankin Bakin Ruwa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Ci gaban, a cewar rahotanni, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane hudu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ayarin gwamnan sun yi karo da ’yan Shi’ar ne a lokacin da suke gudanar da muzahararsu ta mako-mako a Bakin Ruwa da ke kan titin Nnamdi Azikiwe.
Karanta Wannan: Ban janyewa kowa ba a zaben gwamnan Kaduna – Asake
Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, wakilin ‘yan Shi’a a jihar Kaduna, Abdullahi Usman, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu daya daga cikin wadanda aka kashen.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a fitar da sanarwa daga baya.