Jam’iyyar Action Peoples Party ta nemi janye karar da ake yi wa zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
Lauyan jam’iyyar APP, Obed Agu, yana kuma rokon kotun da ta yi watsi da karar da ke kalubalantar nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun, SAN, bai yi adawa da janyewar ba.
Daga bisani Shugaban Kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya yi watsi da karar.
Ku tuna cewa kotun ta fara zama a Abuja ranar Litinin.