A yau Talata ne jam’iyyar APC mai mulki za ta fitar da gwani da zai kasance ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Sai dai, za ta shiga fagen zaɓen fid da gwanin ne, daidai lokacin da ta shiga ruɗani da rarrabuwar kai game da batun ɗan takarar masalaha da goyon bayan mafi rinjayen APC.
Manyan turakun jam’iyyar sun kasa jituwa kan batun, abin da kuma ya yi matuƙar yamutsa hazo sa’o’i kafin babban taron na yau.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ba shi da damar sake tsayawa takara bisa kudin tsarin mulki, kasancewa wannan ce wa’adinsa ta biyu kan karaga.
Sama da delagates 700 ake sa ran su jefa kuri’unsu a yau.
Taron na zuwa na zuwa ne kwanaki biyu bayan kazamin harin bindiga da aka kai kan masu ibada a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Matsalar tsaro da rashin aikinyi da tsadar rayuwa na daga cikin manyan kalubale da ke gaban sabon shugaban Najeriya a 2023.