Bulalaiyar majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu, ya taya zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji na jamâiyyar APC murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar.
Kalu, a cikin wani sako da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya yi fatan Oyebanji ya samu nasara a kan mukaminsa, yayin da ya bukace shi da ya rungumi salon shugabanci na gari.
Yayin da yake yabawa alâummar Ekiti bisa zaben dan takarar jamâiyyar APC, Kalu ya bukaci Oyebanji da ya jajirce kan nasarorin da Gwamna Kayode Fayemi ya samu.
A cewarsa, jamâiyyar APC za ta ci gaba da kara karfi.