Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar gazawa, zafi da bacin rai da rashin tausayin talakawa.
Tsohon Ministan Sufuri ya bayyana haka ne a wasikar murabus dinsa da ya aikewa Shugaban Jamâiyyar APC na Ward 8, Ubima, karamar Hukumar Ikwerre Jihar Ribas, mai kwanan wata 1 ga Yuli, 2025.
Amaechi ya bayyana a baya cewa shi ba dan jamâiyya mai mulki ba ne, inda ya dage cewa babu APC.
A cikin wasikar Amaechi, ya ce matakin nasa ya samo asali ne daga kudurinsa na hada karfi da karfe da sauran âyan Najeriya masu kishin kasa âdomin kubutar da alâummarmu daga cikin kuncin kasa, zafi da radadin da jamâiyyar All Progressives Congress ke nunawa a yanzuâ.
“Bayan tuntubar juna da dama, na gamsu cewa wannan lokaci ne da ya dace a kira ta ta fice saboda jam’iyyar ta kauce daga manyan akidu da suka haifar da kafa ta, don haka ba za ta iya kara karfafa fatan da Najeriya ke da shi na samun makoma mai kyau ba.
Amaechi yana daya daga cikin shugabannin gamayyar jamâiyyun adawa da aka kafa domin tsige gwamnatin shugaba Bola Tinubu mai ci a 2027.