Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya tabbatar da zaɓen Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.
An zaɓi Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan ƙusoshin jam’iyyar da suka halarci taron kwamitin zartarwar APC na ranar Alhamis.
Ranar 17 ga watan Yuli ne tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da babban sakataren APC Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu.
Daga bisani, jam’iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban APC shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.
A ranar 27 ga watan Yuli ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanya sunan Sanata Abubakar Kyari cikin jerin mutanen da ya aika Majalisar Dattawan ƙasar don tantance su.
Tun bayan saukar Abdullahi Adamu ne ake ta raɗe-raɗin cewar Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan na Kano zai iya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban APC.
Gabanin hakan dai ana ta ce-ce-ku-ce kan ko sunan tsohon gwamnan na Kano, kuma ɗaya daga cikin manyan na-hannun daman Shugaba Tinubu, yana cikin waɗanda za a naɗa muƙamin minista, musamman saboda rawar da ya taka tun farko samun nasarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.
Shugaban ƙasar ya sanya sunayen wasu a cikin tsoffin gwamnonin APC, a matsayin waɗanda zai bai wa muƙaman minista a gwamnatinsa.