fidelitybank

APC ta yi tsarin shiyya-shiyya gabanin zaben fidda gwani – Orji Kalu

Date:

Bulaliyar Majalisar Dattawa, Dakta Orji Uzor Kalu, ya yi kira ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta bayyana tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar gabanin zaben fidda gwani na shekarar 2023.

Ya kuma kara nanata cewa zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa ne kawai idan jam’iyyar APC ta maida shi yankin Kudu maso Gabas.

Kalu a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce, samar da tsarin raba jam’iyyar APC a bainar jama’a ya zama dole, domin hakan zai taimaka wajen jagorantar masu neman tsayawa takara a kan turbar da ta dace da kuma daidai da bukatun jam’iyyar.

Kalu ya ce: “Yayin da zaben fidda gwani na shugaban kasa ke gabatowa, batun shiyya-shiyya ya sake zama a tsakiya, kuma kamar yadda aka saba, ana cece-kuce. Jam’iyyar na shirin samar da fom na mukamai daban-daban don haka yana da kyau jam’iyyar a cikin gaggawa ta bayyana shirinta na shiyya-shiyya na masu son tsayawa takara.

“Bayyana ofisoshi na da matukar muhimmanci domin ba wai kawai zai nuna haske a kan turbar ‘yan takara ba, har ma zai ceci jam’iyyar daga rashin jituwar da ba dole ba da kuma kararraki bayan kammala zaben fidda gwani.

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp