Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi nasarar lashe zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisar tarayya da aka gudanar a jiya Asabar, kamar yadda hukumar zaɓe ta bayyana.
Baturen zaɓe Fafesa Salisu Ibrahim ya ce Rabiu Mukhtar na APC ne ya lashe zaɓen na mazaɓar Garki-Babura da ƙuri’a 38,449.
A cewar baturen zaɓen, ɗantakarar jam’iyyar PDP Auwalu Isa ne ya zo na biyu bayan ya samu ƙuri’a 13,519.
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe duka zaɓukan cike gurbi uku da aka gudanar a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, kamar yadda hukumar zaɓe ta Inec ta sanar.
Sakamakon da aka gudanar a mazaɓar majalisar tarayya ta Chikun/Kajuru ya nuna cewa Felix Bagudu na APC ɗin ya samu ƙuri’a 34,580 kuma ya doke na PDP da ya zo na biyu da ƙuri’a 11,491.
Kazalika, APC ta yi nasarar cin zaɓen ‘yanmajalisar jiha na mazaɓun Zaria/Kewaye da kuma Basawa.
Baturen zaɓe na Zaria Kewaye Balarabe Abdullahi ya sanar cewa ɗantakarar APC Haruna Ihamo ne ya cinye da ƙuri’a 26,613, yayin da abokin hamayya na SDP Nuhu Sada ya samu 5,721.
A zaɓen Basawa kuma, baturen zaɓe Farfesa Nasiru Rabiu ya ce APC ta samu ƙuri’a 10,926 kuma ta doke PDP mai 5,499.
Da ma APC ce ke mulkin jihar ta Kaduna bayan ɗantakararta Uba Sani ya lashe zaɓen gwamna na watan Maris ɗin 2023.