Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya gargadi Bashir Machina, da ke cewa shi ne dan takarar sanata mai wakiltar Yobe ta arewa a Apc, a kan ya shiga taitayinsa.
Abdullahi Adamu, ya yi wannan gargadin ne a yayin da yake kare matakin da jam`iyyarsu ta dauka na mika sunan shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ga hukumar zabe a matsayin dantakarar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa maimakon Bashir Machina.
Shugaban jam’iyyar ta APC, ya gargadi Machina da cewa, ya yi hattara domin maganganun da yake faɗa sun fara neman su yi yawa.
Ya ce,” Ni a matsayina na shugaba na san babu wata doka da jam’iyya ta karya, domin babu wata doka da ta ce, idan ka shiga wata takara ba za ka shiga wata ba, don haka ba dokar da ta hana shi ko ta hana kowa ma.”