Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da haddasa rashin hadin kai a Najeriya.
Dan jam’iyyar PDP ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘ya’yan jam’iyyar PDP, inda ya bukaci jam’iyyar reshen jihar Legas da ta hada kai domin samun damar mamaye jihar Legas.
Atiku ya ce, “mu sheda ne kan kalubalen da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta jawo mana a kasar nan.
“Babban kalubalen da APC ta kawo shi ne rashin hadin kai. Ba a raba mu haka a baya ko a lokacin yakin.
“Muna da alhakin korar jam’iyyar amma dole ne mu hada kai domin mu samu damar yin hakan. PDP ta yi fama da rashin hadin kai tsawon shekaru.
“Ina kira ga PDP ta Legas da ta kawo hadin kai a jam’iyyar. Ina kira ga babba da don Allah a tabbatar da hadin kai a jam’iyyar reshen jihar Legas domin mu karbi mulkin jihar.