A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, aka kammala tantance shi a matsayin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.
Okorocha dai ya kammala tantance shi ne bisa shakkun ba zai yi hakan ba, biyo bayan kama shi da tsare shi da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta yi masa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama tsohon gwamnan na jihar Imo, kuma ana tsare da shi tun ranar Talata, bisa zargin zamba.
A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya ta bayar da belinsa a kan kudi naira miliyan 500, daga nan ne kotun Abuja ta bayar da umarnin cewa hukumar EFCC ta lallasa Sanatan Imo ta Yamma kuma a ci gaba da tsare shi har sai an cika sharuddan belinsa.
Sai dai Okorocha cikin rashin jituwa ya halarci bikin tantancewar, bayan da ya mika godiyarsa ga magoya bayansa da suka tsaya masa, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na bukatar shugaban kasa irinsa da zai jagoranci al’amuran kasa.
Da yake magana a kan lamarinsa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa, tsohon gwamnan jihar Imo ya yi alkawarin yin jawabi ga manema labarai nan da kwanaki masu zuwa.
Ana sa ran gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da na kasa tsakanin 6 zuwa 8 ga watan Yunin 2022.