fidelitybank

APC ta samu ƙaruwa a zauran majalisar dokokin Kano

Date:

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birni a majalisar dokokin jihar Kano, Salisu Ahmad Gwangwazo, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a ranar Juma’a.

Dan majalisar ya bayyana matakin nasa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Hamisu Chidari a Kano. majalisar, Malam Uba Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Ahmad-Gwangwazo ya sanya rabe-rabe a shugabancin jam’iyyar PDP a matakin jiha da kasa a dalilin sauya shekarsa.

Sakataren yaɗa labaran majalisar, Malam Uba Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Ahmad Gwangwazo ya sanya rabe-rabe a shugabancin jam’iyyar PDP a matakin jiha da kasa a dalilin sauya shekarsa.

Ya bayyana cewa a cikin wasikar da dan majalisar ya aike wa kakakin mai taken: “Sanarwar sauya shekata daga PDP zuwa APC’, ya mika cewa bangaran ya sanya ba zai yiwu a ci gaba da gudanar da ayyukan jam’iyyar ba.

Abdullahi ya kara da cewa Chidari ya taya Ahmad-Gwangwazo murnar shiga jam’iyyar APC tare da tabbatar masa da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da tafiyar da shi da magoya bayansa a kowane hali.

Shugaban majalisar ya kuma tabbatar da cewa, jam’iyyar na gudanar da tsarin da ya kunshi kowa da kowa, ya kara da cewa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar suna da ruwa da tsaki a ci gaban jihar.

Abdullahi ya kuma ruwaito shugaban majalisar na cewa akwai alamun jam’iyyar APC mai mulki za ta ci gaba da rike madafun iko a jihar a zaben 2023 mai zuwa.

Bayan sauya shekar Ahmad-Gwangwazo, majalisar tana da ‘yan majalisar APC 20 da kuma 11 na PDP.

fg spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp