Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna damuwa a kan shirin da hukumar zaɓe ke yi na aiki da na’urar tantance masu zaɓe da aika sakamako ta intanet da ake kira BVAS a babban zaɓen da ke tafe.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 93 a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya.
Shugaban Jam’iyyar ta APC ya ce yana shakkar ko bullo da tsarin amfani da na’aurar ta BVAS zai samar da kyakkyawan sakamako ga al’ummar kasar baki daya a zaben 2023.
A cewarsa Najeriya ba ta shirya amfani da wannan fasaha a lokacin zabe ba amma kuma ya ce idan za a yi to ya zama wajibi ga hukumar zabe ta tabbatar wa ‘yan Najeriya ta shirya dari bisa dari don ta gamsar da kowa da kowa.
Bala Ibrahim shi ne Darakatan yada labaran Jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa damuwa shugaban jam’iyyar ya nuna a kan tasirin naurar wajen samar da sahinin zabe : “ Damuwa ce ga niyya ko kuma ganin an yi adalci ga kowa da kowa.”
“ Akwai wasu wurare wadanda a halin da ake ciki yanzu naurar ba ta aiki, wannan waya ta hannu akwai inda ba ta aiki.”