Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kafa kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun mai wakilai 86 da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Yuli.
Jam’iyya mai mulki ta nada Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Legas, ya jagoranci tawagar mutane 86.
A sanarwar da suka fitar ranar Talata, Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore, shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma sakatare, sun ce za a kaddamar da majalisar yakin neman zaben a sakatariyar jam’iyyar ta kasa ranar Alhamis.
Sanarwar ta kara da cewa, “Za a gudanar da taron kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni, 2022 da karfe 2:00 na rana a shelkwatar APC ta kasa, Abuja.