Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya roki jam’iyyar APC da ta tsayar da tikitin takarar shugaban kasa a yankin Kudancin ƙasar nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin wata sanarwa mai taken, “Dole jam’iyyarmu ta APC ta bi tafarkin daidaito” a Akure, babban birnin jihar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, shugabancin jam’iyyar ya tabbatar da cewa, tsarin wakilcin karba-karba ne ya jagoranci shawarar ta a babban taron da aka kammala.