Jam’iyyar APC mai mulki, ta shaidawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, cewa ba gudu ba ja da baya kan manufofin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanya a gaba, za kuma su ci gaba da goyon bayan shi kan farfado da kyakkyawan fatan ‘yan Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito APC na nanatawa PDP babu wani magudi da aka yia zaben gwamna da aka yi a jihar Edo makonnin da suka gabata, wanda jam’iyyar PDP ami mulki ta sha kaye a zaben da aka yi.
Jam’iyyar ta yi watsi da jita-jitar gwamnatinsu na son maida siyasar kasar ta jam’iyya daya, da salon mulkin kama karya.
Daily Trust ta ce a ranar Alhamis ne dai kwamitin amintattun jam’iyyar adawa ta PDP, ya zargi APC da kulla mkarkashiya a zaben da aka yi na jihar Edo,
Da ya ke jawabi ga manema labarai bayan taron na kwamitin amintattu, shugaban kwamitin, Sanata Adolphus Wabara, ya bayyana damuwa kan yadda lamura ke kara tabarbarewa a Najeriya musamman matsin tattalin arziki, da tsadar rayuwa da ya dora hakkin hakan kan gwamnatin Tinubu.
A dai ranar Laraba ‘yan Najeriya suka tashi da karin farashin man fetur a karo na biyu cikin wata guda da babban kamfann mai na kasa NNPC ya yi.