Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola, sun kammala shirye-shiryen shigar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da jm’iyyar PDP ta Jihar da kuma zababben Gwamnan Jihar, Sanata Ademola Adeleke zuwa kotun sauraron kararrakin zabe.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Gboyega Famodun ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar a Osogbo, ranar Alhamis.
Sanata Ademola Adeleke shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar 16 ga watan Yuli inda ya doke dan takarar jam’iyyar APC kuma gwamna mai ci, Adegboyega Oyetola.
Famodun ya ce, lauyoyin jam’iyyar da na Gwamna Adegboyega Oyetola sun kammala shirye-shirye kuma za su kai kara kotu.
Ya kara da cewa, lauyoyin sun shaida musu cewa, “muna da kwakkwarar hujja kuma mun yi imanin za mu yi nasara a kotu.”


