Hukumar zaɓen jihar Kogi ta ayyana jam’iyyar APC mai mulkin jihar a matsayin wadda ta lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 21 da kuma na kansiloli 239 da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban hukumar zaɓen jihar, Mamman Nda-Eric wanda ya ayyana haka, ya ce zaɓen ya gudana cikin gaskiya da adalci ba.
Gwamnan jihar ta Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen da kuma ƴan jihar da suka kasance cikin tsanaki tare da zaɓar abin da suke so ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.
Sai dai jam’iyyu adawa a jihar irinsu PDP da CNPP sun yi zargin cewa abin da aka yi a matsayin zaɓe, abin kunya ne ga dimokraɗiyya.
Sun ce ba a gudanar da wani zaɓe ba a jihar, inda suka ce hukumar zaɓen jihar ta sake nuna gazawarta wajen shirya sahihin zaɓe.