Jamâiyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe dukkan kujerun shugabanni 27 da kansiloli 312 a zaben kananan hukumomin jihar Borno da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Borno, BOSIEC, Alhaji Lawan Maina ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben da aka gudanar ranar Lahadi a Maiduguri.
âBayan gudanar da zaben a ranar Asabar, a yau mun samu sakamako daga kananan hukumomi 27 kamar yadda doka ta ba mu a karkashin sashe na 10.
âA matsayina na babban jamiâin yada labarai na jiha, na karanta sakamakon kamar haka:-
âJamâiyya mai mulki, APC ta lashe dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar 27.
âHakazalika, jamâiyya mai mulki ta lashe dukkan kansiloli 312 (kansiloli) a daukacin kananan hukumomin jihar.
“Da wannan, mun zo karshen wannan atisayen kuma za a gabatar da takardar shaidar ga wadanda suka yi nasara a wani lokaci da za a bayyana nan ba da jimawa ba,” in ji Maina.