Jam’iyyar APC mai mulki ta ce, ta shirya tsaf domin soma gangamin yakin neman zabenta na 2023.
Gwamnan Filato wanda shi ne shugaban gangamin yakin neman zaben shugaban kasa ta APC, Simon Lalong, ya sanar da hakan ne bayan kammala sa ido kan gyara ofishin gangamin yakin neman zabensu da ke Abuja.
Gwamnan ya kuma gana da wasu ma’aikatar kwamitin yakin neman zaben, a kokarin tabbatar da cewa komai ya tafi daidai.
Ya kuma samu ganawa da ɗan takarar shugabancin kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a hedikwatar.


