Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a Afrika.
Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake maraba da tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, zuwa jam’iyyar, yana mai jaddada cewa “babban alheri ne”.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Edwin Olofu ya fitar a ranar Lahadi, Ganduje ya ce kwarewar Anyim zai yi amfani ga APC.
Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, tun da farko Ganduje ya karbi Anyim, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC a wani biki da aka yi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Da yake jawabi, Ganduje ya ce: “Na yi farin ciki da karbar irin wannan muhimmin mutum a cikin jam’iyyarmu.
“Ina so in tabbatar muku a madadin Shugaba Bola Tinubu cewa, maraba da ku zuwa babbar jam’iyyar siyasa a Afirka.
“Ku tabbatar da cewa za mu ba ku dama daidai gwargwado kamar tsofaffin ’yan jam’iyyarmu domin ku zo kan tebur tare da dimbin gogewa da bin diddigin ku.”


