A wani yunkuri na sasanta rikicin da suka taso daga majalissar dokokin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na ‘yan takara a jihar Oyo gabanin zaben 2023, jam’iyyar ta kafa kwamitin sulhu na mutum 24.
Shugaban jam’iyyar a jihar Isaac Omodewu ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Asabar a sakatariyar jam’iyyar dake Oke-Ado, Ibadan, babban birnin jihar.
Shugaban kwamitin sulhun shi ne Cif Olufemi Lanlehin yayin da Sakataren shi ne Alhaji Tajudeen Olanite.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Hadji Dr Ameed A Ayinde, Hon Lasun Adebunmi, Alhaji Gbadamosi Abu Adejare, Cif Timothy Alarape Jolaoso, Injiniya Oladayo Lawal, Cif Badmos Bukola, Sunday Ajadi, Hon Chief S. O. Olaoye, Balogun Gaphar Oyetola da Erelu Funke Olayanju.
Pastor Adewale Adepoju, Alhaji Kakako Ayinla, Alhaji Ramon Aderemi Sadiq, Hon Olorode Samuel Oluade, Otunba Kunle Folarin, Akande Abass, Alhaji Kareem Adebayo, Dr Adepeju Esan, Tunde Ajibola, Remi Olalekan, Injiniya Oke Kolawole da Hafeez Omobolaji Repete.
Da yake kaddamar da kwamitin, Shugaban jam’iyyar APC na Oyo ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su bai wa kwamitin hadin kai don ganin an shawo kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.