Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ‘ya’yan jam’iyya mai mulki sun sasanta matsalolin cikin gida.
Tinubu ya bayyana haka ne a Ado-Ekiti a ranar Talata a wani babban gangami da aka gudanar domin tantance kuri’un dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Biodun Abayomi Oyebanji, gabanin zaben ranar Asabar a jihar.
Ya bayyana cewa, jam’iyya mai mulki ta sasanta bambance-bambancen da ke tsakanin ta, kuma a yanzu ta hade kai don samun nasara a zaben gwamnan Ekiti da kuma ci gaba da rike madafun iko a cibiyar a 2023.
Tinubu ya yabawa Buhari kan yadda ya goyi bayan yunƙurin dawowar mulki yankin Kudu a 2023 tare da bayyana shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC don haɗa kan ƙasar.