Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce za su dorawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) jagorancin gwamnatin tarayya alhakin gazawar su.
Atiku a wata sanarwa da ya rabawa magoya bayan sa, Lahadi ya bayyana zaben 2023 a matsayin kuri’ar raba gardama kan ayyukan jam’iyyar APC.
Ya ce jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, suna son guduwa daga gazawar su, amma PDP ba za ta bar su ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “A kasar Benin jiya, na bayyana tsare-tsarena a fili kan ayyukan da ke gabanmu na hada kai, ceto, da dawo da Najeriya.
“Shiri ne da ya kunshi dimbin kalubalen da ke damun mu a halin yanzu, kuma babban makasudin yakin neman zabe shi ne tallata wadannan tsare-tsare ga ‘yan Najeriya.
“A gare ni da duk wanda ke bangaren PDP har da ku, babban zabe mai zuwa shi ne zaben raba gardama kan ayyukan jam’iyyar APC.
“Jam’iyya mai mulki za ta so ta gudu daga rashin aikin da suke yi. Hasali ma, za su yi fatan mu mai da hankali kan batutuwan da ba su da nasaba da zabe mai zuwa. Amma ba za mu ba su wannan damar ba. Za mu yi musu hisabi a kan sakamakon da suka samu.
“Amma ko da hakan bai isa ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne kada mu sake yin kuskure iri ɗaya.
“Don haka ya zama wajibi a gare mu mu tantance tsare-tsaren kowace jam’iyyar siyasa mu bar hakan ya zama ma’auni na shawarwarin zaben mu”.
Atiku ya ba da tabbacin cewa a matsayinsu na dan takarar shugaban kasa na PDP, za su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi zabe mai zuwa.