fidelitybank

APC ta fadi dalilin da ya sa ba ta rantsar da shugabannin jami’ya na Kano ba

Date:

 

 

Uwar Jam’iyar APC ta Ƙasa ta faɗi dalilin da ya sanya ba ta rantsar da shugabannin jam’iyar na Jihar Kano ba.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Alhamis da ta gabata ne dai jam’iyar ta rantsar da shugabannin jam’iya na jiha a jihohi 34 amma banda Kano da Sokoto.

Da ya ke bayani a kan dalilan da ya sanya ba a rantsar da shugabannin jam’iya na Kano ba, Sakataren Kwamitin Riƙo na APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe, ya ce babu wani abin damuwa a kan matakin.

A cewar sa, uwar jam’iyar ta ɗauki matakin dakatar da rantsar da shugabannin jam’iya na Kano ne domin amfanin ƴan jam’iyar, jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ya ce APC na son zaman lafiya kuma Kano ta zama kamar nan ne Shalkwatar jam’iyar, inda ya ce ba za a yi wani abu da zai kawo naƙasu ga zaman lafiyar jam’iyar a jihar ba.

Akpanudoedehe ya ƙara da cewa akwai maganar shari’ar jam’iyar a kotu, sabo da haka uwar jam’iyar ba a ta yi wani abu na kuskure ba.

Sai dai kuma bai fadi dalilin da ya sanya ba a rantsar da shugabannin jam’iya na Sokoto ba

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...

Kano na cikin jihohin da ba su yi katin zabe sosai ba – INEC

Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya...

Mun gano filin wasa na Sani Abacha ba shi da inganci – NPFL

Hukumar shirya gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL),...

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya ya fadi

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji da ya taso daga...

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...
X whatsapp