Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin jihar Kaduna a mazabar Sanga.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Haliru Dangana a matsayin wanda ya lashe zaben.
Jami’in zabe na INEC, Farfesa Umaru Musa ne ya sanar da sakamakon a Gwantu, a daren Asabar.
Karanta Wannan: Wamako ya lashe kujerar Sanata a Sokoto
Dangana ya samu kuri’u 13,883 inda ya doke Comfort Amwe na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 13,275.
“Haliru Dangana na jam’iyyar APC, bayan da ya cika sharuddan doka ta hanyar samun kuri’u mafi girma an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji Musa.


