Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta dakatar da dan majalisar wakilai Aminu Jaji, bisa wasu zarge-zarge da cin dunduniyar
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wata ganawa da manema labarai a Gusau ranar Juma’a.
Aminu Jaji yana wakiltar mazabar tarayya ta Kaura-Namoda da Birnin-Magaji a majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC.
Sai dai sakataren APC, Yusuf Idris, ya ce, wasu zarge-zargen da ake yi wa Jaji sun hada da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.
Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Dan majalisar Aminu Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Birnin-Magaji bisa zargin cin hanci da rashawa da dai sauransu.
Sai dai kuma Aminu Jaji ya ce, shugabancin jam’iyyar APC na jihar, ba su bi ka’idojin tsarin mulki na jan ragamar jam’iyyar.