Bangarorin biyu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Abia, sun kawo karshen rikicin shugabancin da suka shafe shekaru takwas suna yi, tare da bayyana cewa “babu mai nasara, ba wanda ya ci nasara”.
Biyo bayan rikicin shugabanci da ya barke tsakanin tsohon shugaban jihar Cif Donatus Nwankpa da wani jigo a jam’iyyar Cif Ikechi Emenike, jam’iyyar ta koma gida-gida a shekarar 2014.
A shekarar 2015 bangaren Nwankpa ya gabatar da Cif Anyim Nyerere a matsayin dan takarar gwamna a kan Emenike, wanda ya tsaya takarar gwamna a karkashin Dr Emmanuel Ndukwe a matsayin shugaban kungiyar.
Jam’iyyar ta kuma gabatar da ‘yan takarar gwamna guda biyu tare da shugabannin bangarorin biyu a shekarar 2019, inda tsohon ministan ma’adinai da karafa, Cif Uche Ogah ya fafata da Emenike.