fidelitybank

APC shiyyar Arewa ta kudiri aniyyar mara wa Tinubu da Shettima a 2023

Date:

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) shiyyar Arewa maso Yamma, sun kuduri aniyar amincewa da zaben tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

An dauki wannan kudiri ne a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, lokacin da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (Arewa maso Yamma), Salihu Moh Lukman, ya jagoranci masu ruwa da tsaki a rangadin yankin.

Sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Musa Mailafiya Mada, ya fitar a Abuja bayan kammala rangadin, ya bayyana cewa sun kuma tattauna dabarun kawo nasara a jam’iyyar.

“Batun daga cikin batutuwan da aka tabo a taron shi ne fitowar Kashim Shettima a matsayin abokin takarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Tinubu da kuma yadda ya kamata shiyyar ta tsayar da kanta wajen kawo wa jam’iyyar nasara a dukkan matakai.

Mahalarta taron sun kuduri aniyar yin aiki da hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar tare da kara himma wajen zaburar da ‘yan Najeriya su zabi Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasar Najeriya da kuma dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023. karanta.

leadership newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp