Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya ce, hanyar samar da yarjejeniya da aka amince da ita a babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata ya kara wa jam’iyyar hadin kai da kuma kara karfi.
Ya ce, an samu nasarar gudanar da taron ne, sakamakon shawarwarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar game da tsarin yarjejeniya.
“Haka zalika babban nasara ne idan aka duba hanyoyin da aka bi, domin fito da wannan tsarin. Na san kuna sane da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarce mu da mu ci gaba da tafiya tare,” in ji Ganduje a wata sanarwa da kakakinsa, Abba Anwar ya fitar.
“Ko da a cikin yanayin da yarjejeniya bai yi tasiri ba, dole ne su shiga zaben tare da dukkan hanyoyin da suka dace,” in ji gwamnan.
Ganduje ya kuma yi nuni da cewa APC ta fito da sabon salon shugabanci, inda ya kara da cewa hakan ya kara wa jam’iyyar hadin kai da kuma kara karfi.