fidelitybank

APC na zawarcin Kwankwaso da mabiyansa – Ganduje

Date:

Jam’iyyar APC mai mulki ta shiga zawarcin kananan jam’iyyun adawa ciki harda NNPP ta Rabi’u Musa Kwanwkaso da mabiyansa.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shaida wa BBC cewa tuni suka aike da goron gayyata ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya yi waÉ—annan kalamai ne a wani taro da ya jagoranta da shugabannin jam’iyyarsa ta APC a jihar Kano, inda ya ce dama can uwa É—aya uba É—aya suke da su Kwankwason.

A cewa Ganduje, “Wannan ya zama dole saboda a matsayina na shugaban jam’iyyar APC na kasa ina zagayawa jihohi, sanatoci sun shigo cikin wannan jam’iyya tamu ‘yan majalisar tarayya sun shigo wannan jam’iyya tamu, haka nan kuma gwamnoni.

Shugaban APC ya ce nan gaba ma akwai wadanda za su shigo cikin jam’iyyar, kuma wannan dalili ne ya sa ya fito yana neman hadin kai daga jiharsa ta Kano.

“Na ma kira wasu na waje ballantana namu na gida” in ji shi.

Sai dai shugaban jam’iyyar APC ya ce kawo yanzu ba su rubutawa jagoran jam’’iyyar NNPP da gwamnan jihar Kano wasika a hukumance ba game da wannan kiran da suka yi mu su.

A cewarsa suna son É“angaren Kwankwaso ya nuna sha’awar shiga jam’iyyarsu ta APC kafin a je matakin aike wasika.

Wannan bukata ta APC na zuwa ne adaidai lokacin da jama’a da dama ke nuna shaku kan ba lallai tafiyar tayi kyau ba tsakanin Kwankwaso da Ganduje a inuwa guda.

Amma Ganduje ya nuna kwarin gwiwa tare da tunasar da cewa, “ai dama can gidanmu É—aya, dama can Ubanmu É—aya, an samu rarrabuwar kai, yanzu kuma idan Allah ya sake haÉ—awa, to me ya fi wannan daÉ—i”.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar Æ´an Æ™asarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp