fidelitybank

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Date:

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da taron ƙoli, karo na farko gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.

Mahalarta taron, wanda ke gudana a yau Alhamis su ne Shugaban ƙasar, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da kuma shugabannin Majalisar Dattaijai da Wakilai da mataimakansu.

Haka nan gwamnonin jam’iyyar masu ci da kuma tsofaffi suna cikin waɗanda aka gayyata domin halartar taron.

Wannan na zuwa ne gabanin cikar shugaban na Najeriya shekara biyu da kama mulki, daidai lokacin da ake ganin jam’iyyar na ƙara samun tagomashi sanadiyyar tuɗaɗar ƴan adawa zuwa cikin jam’iyyar daga sauran jam’iyyu.

Jam’iyyun adawar ƙasar da dama na fama da rikicin cikin gida, ciki har da babbar jam’iyyar adawa ta ƙasar – PDP, wadda ake kyautata zaton ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar ya kammala tattaunawar yin haɗaka da wasu manyan ƴan adawa a wata jam’iyyar ta daban.

Jam’iyyun adawar na zargin APC da yi wa ƴan adawar alƙawurra masu gwaɓi domin janyo su zuwa cikinta, lamarin da jam’iyyar ta sha musawa.

Sanarwar taron ƙolin na APC ta ce, ɗaya daga cikin abin da za a tattauna shi ne duba manufofin Tinubu tun bayan kama mulki.

Shugaba Tinubu dai ya bijiro da sabbin manufofi a ƙasar daga ranar da aka rantsar da shi, inda wasu daga cikinsu suka sauya lamurran ƙasar.

Al’ummar ƙasar sun koka kan faɗawa cikin rayuwa mai tsanani bayan cire tallafin man fetur da kuma wasu matakai da gwamnatin ta ɗauka a fannin tattalin arziƙi.

Haka nan matsalar tsaro na ci gaba da addabar yankunan ƙasar duk da matakan da gwamnatin ke cewa tana ɗauka.

Sai dai masu kare gwamnatin na cewa matakan da shugaban ya ɗauka a fannin tattalin arziƙi za su yi amfani ga ƙasar a nan gaba.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Isra’ila ta kashe mana fararen hula – Syria

Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya zargi Isra'ila da kai...

Za mu koma fadar gwamnatin Katsina mu karbi gaisuwar Buhari – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ce bayan...

Tinubu zai jagoranci yi wa Buhari addu’a

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, zai jagoranci taron addu'o'i na...

Muƙarraban Buhari sun ci amanar da ya ba su lokacin mulkinsa – Bagos

Wani tsohon ɗan majalisar wakilai, Dachung Bagos ya bayyana...

Guardiola ya bude kofa ga ‘yan wasa shida su bar kungiyar

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, a shirye yake ya...

Ba gudu ba ja da baya a zanga-zangar mu – Tsofaffin ‘Yansanda

Kungiyar ‘yan sandan Najeriya masu ritaya ta sanar da...

Malami ya magantu kan sukar rashawa a mulkin marigayi Buhari

Tsohon babban Lauyan Najeriya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami,...

Turkiyya ta gargadi Najeriya kan ‘yan ta’addar FETO

Gwamnatin Turkiyya ta fitar da wani gargadin cewa, mambobin...

Kiristoci sun jinjinawa Musulmai yadda aka yi jana’izar Buhari ba kashe kudi

Ana samun karuwar al’ummar Kudancin Najeriya musamman mabiya addinin...

An binne marigayi Muhammadu Buhari a gidansa na Daura

An binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a...

Pillars ta dauki yan wasa guda biyu

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta tabbatar da...

An cafke ‘yan Daba 28 a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu...
X whatsapp