Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya na rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi a birnin tarayyar Abuja.
Wannan na zuwa ne makwanni kadan gabanin taron gangamin APC da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairu.
An samu tsaiko a wasu lokuta yayin gudanar da tarukan gangamin jam’iyyar a jihohi daban-daban na APC a Najeriya.
Rahoton da muke samu daga jaridar TheCable na cewa, a halin yanzu an tsaurara tsaro a sakateriyar jam’iyyar APC ta kasa dake babban birnin tarayya (FCT). Wannan mataki na zuwa ne daidai lokacin da Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar, zai kaddamar da shugabannin jihohi a yau Alhamis 3 ga watan Fabrairu.