A ranar Talata ne ake sa ran kwamitin da ke tantance masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Jam’iyyar APC, John Oyegun, zai ci gaba da tantance sauran masu neman tsayawa takara.
Ranar Litinin ne kwamitin ya fara tantance masu neman takarar.
Ana tantance masu neman takarar ne gabannin gudanar da zaɓen fitar da gwanin da za a gudanar na jam’iyyar tsakanin shida zuwa takwas ga watan Yunin 2022.
Ana gudanar da aikin tantancewar ne a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Cikin waɗanda aka tantance a karon farko akwai tsohon gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru da tsohon Ministan Sufuri Chibuike Amaechi da tsohon Gwamnan Ogun Ibikunle Amosun.
Sauran sun haɗa da tsohon ƙaramin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba da Gwamnan Ebonyi Dave Umahi da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani da tsohon Gwamnan Zamfara Sani Yarima.