Jam’iyyun siyasar Najeriya tun daga jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar hammaya wato PDP sun ce, sun kammala shiri domin fafatawa a zaɓen fid da gwani cikin wa’adin da hukumar zaɓen ƙasar ta ƙayyade.
Jadawalin zaɓen 2023 ya nuna cewa, jam’iyyun ƙasar za su yi zaɓukan fitar da gwanayensu ne daga ranar 4 ga watan Afrilu har zuwa ranar 3 ga watan Yuni.
Zaɓukan fid da gwanin, wani mataki ne na tunkarar babban zaɓen na 2023.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce, jam’iyyun da ke son shiga zaben 2023 a hukumance za su iya gudanar da zaben fid da gwani tun daga ranar 4 ga watan da muke ciki har zuwa 3 ga watan Yuni.