fidelitybank

APC ba ta tsoron hadakar abokan hamayya – Orji Uzor Kalu

Date:

Sanata mai wakiltan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba ta tsoron jam’iyyar adawa.

Kalu ya ce gamayyar jam’iyyun adawa na da ‘yancin kalubalantar jam’iyyar APC, amma jam’iyya mai mulki za ta ci gaba da mai da hankali wajen gudanar da ayyukan ta.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ke jagorantar kafa kungiyar hadin gwiwa.

Gamayyar a cewar El-Rufai za ta tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya fadi zaben shugaban kasa a 2027.

Sai dai tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara yaba ayyukan gwamnatin APC da ta mayar da hankali kan harkokin mulki.

Kalu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Talata.

Ya ce: “Ba mu yi barci ba, APC ba ta da dalilin tsoro, mu ne jam’iyya mai mulki kuma mai kishin ci gaban Nijeriya.

“Da yawa daga cikinmu muna saka hannun jari a masana’antu don samar da ayyukan yi fiye da siyasa.

“Wadannan amincewa ba wai tsoro ba ne, sakamakon jajircewar shugaban kasa ne ya yanke shawara da kawo sauyi.

“’Yan adawa suna da ‘yancin kalubalantarmu, aikinsu kenan, amma mu namu shine samar da sakamako, kuma muna yin haka.

“A cikin lokaci mai tsawo, ‘yan Najeriya za su fahimci zabukan da wannan gwamnatin ta yi.”

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp