Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa, ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki, mutane ne masu son kai kawai, wadanda suka damu da kansu kawai, iyalansu, abokansu da makarrabansu domin cutar da galibin ‘yan Najeriya.
Gwamnan ya yi wannan zargin ne a filin wasa na garin Misau a ranar Asabar din da ta gabata a ci gaba da rangadin yakin neman zabensa na kananan hukumomi 6 da ke da mazabar Bauchi ta tsakiya domin neman sake tsayawa takara a karo na biyu.
Mohammed ya ce, “Jam’iyyar APC mai son kai ce, ‘ya’yanta masu son kai ne kuma suna kula da kansu da iyalansu kawai.”
A fusace Gwamnan ya ce, “Sun yaudare mu kuma hakan ya faru ne saboda ba mu da haɗin kai. Don haka muna bukatar mutane irin ’yan takara na yanzu a PDP su canza labari zuwa ga alheri.”
Ya koka da cewa babu wani aiki ko daya da ‘yan majalisar tarayya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke wakiltar jihar Bauchi suka gudanar tun lokacin da shi da Ahmed Abdul Ningi suka bar majalisar.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa dukkan ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata duk an yi su ne da yardar al’ummar al’ummar da suka amfana.
Ya bayyana cewa, “Na zo nan (Misau) ta Gwaram, Hardawa kuma mutanen Bauchi ta tsakiya sun nuna soyayyar PDP kuma ba mu da wani zabi illa mu ci gaba da yi muku adalci.
An yaba wa Gwamnan da dimbin ayyukan more rayuwa da ci gaban bil’adama da ba a taba ganin irinsa ba da aka raba a kananan hukumomi 20 na jihar tun bayan hawansa mulki a Nat 2019 wanda masana ke ganin zai kara masa damar sake tsayawa takara.
Ya jaddada cewa “Mun gudanar da dukkan ayyuka da shirye-shiryen karfafawa tare da amincewar mutanenmu saboda sun san inda takalman ke tsinke.”
Ya ce ayyukan gina tituna da ruwan sha da gine-gine da gyara makarantu da asibitoci da karfafa gwiwar jama’a an yi su ne bisa la’akari da irin matsalolin da al’umma ke ciki a jihar.