Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya baiyana cewa babu bambanci tsakanin jami’ya mai mulki APC da ta adawa, PDP.
Shekarau, Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, ya baiyana hakan ne a yau Lahadi a Sokoto yayin ƙaddamar da wani shiri na tallafi da ga dan majalisar wakilai, Balarabe Salame (APC- Gwadabawa/Illela).
A cewar Shekarau, a duk jam’iyyun da ke ƙasar nan, a kwai mutanen da su ke da kyakkyawar niyyar a kan talakawa.
Hakazalika, in ji Shekarau, a su waɗannan jam’iyyun, a kwai mutanen da ba talakawa ne a gaban su ba sai dai buƙatar su kawai su ka sa a gaba.
Shekarau ya ja hankalin al’umma cewa su dage su riƙa tabbatar da cewa mutanen da za su zaba na kirki ne da za su ciyar da su gaba.
Ya kuma yaba wa tsarin siyasar Sokoto, inda ya yi kira ga sauran jihohi su kwaikwaya.
“A ce gwamna a jam’iyar PDP ya zo taron da ɗan majalisa a ƙarƙashin APC ya shirya, kuma ga shugabannin duka jam’iyu da sauran magoya baya sun halarci taron, wannan abin yabawa ne matuƙa,” in ji Shekarau.