Sabon zababben shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyya mai mulki a shirye take ta karbi bakuncin shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Rabiu Kwankwaso, idan har yana so ya sauya sheka.
Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana matsayar sa a yayin tattaunawa da wasu zababbun kungiyoyin yada labarai a Kano a daren ranar Asabar.
Shugaban jam’iyyar APC ya bayyana cewa a yanzu shi ne ke tafiyar da al’amuran jam’iyyar, inda ya jaddada cewa matsayinsa ya sa Kwankwaso ya samu saukin komawa jam’iyyar mai mulki idan ya so.
Ya bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasa nagari wanda ya rike mukamai da dama a jihar da kasa baki daya.
Ya ce: “Ba wanda zai ce Kwankwaso ba dan siyasa ba ne; aƙalla ya kasance gwamnan Kano na wa’adi biyu, duk da cewa a cikin wa’adin mulkinsa ya lalace; ya kasance Ministan Tsaro, duk da cewa bai san menene tsaro ba; kuma ya taba zama Sanata, duk da cewa bai taba cewa komai ba tsawon zamansa a wurin.
“Amma idan har yana son sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, kofar mu a bude take, musamman a yanzu da wani dan jiharsa ya zama shugaban jam’iyyar; zai yi masa sauki ya shiga harabar,” ya kara da cewa.